Najeriya: Dangote Ya Fara Saida Tataccen Man Fetur Da Dalar Amurka

Matatar man fetur da gas ta Dangote a tarayyar Najeriya ta fara sayar da man fetur da dangoginsa da dalar Amurka, ta kuma daina karban

Matatar man fetur da gas ta Dangote a tarayyar Najeriya ta fara sayar da man fetur da dangoginsa da dalar Amurka, ta kuma daina karban naira na Najeriya.

Jaridar Daily Trust ta Najeriya ta nakalto majiyar kamfanin dangote na cewa ya dauki wannan matakin ne saboda yanda chanjin dalar Amurka yake sassauyawa daga lokaci zuwa lokaci.

Labarin ya kara da cewa daga yanzun za’a ci gaba da sayar da tataccen man fetur, gas na girki da kuma man desel ko da laranzin duk da dalar Amurka.

Masana suna ganin daga yanzun kuma farashin man fetur da dangoginsa a cikin kasar zai kasance kan farashin dalar Amurka a kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted