Najeriya da Angola sun rattaba hannu kan yarjejeniyar cire biza ga masu fasfo na diflomasiyya

Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Ambasada Yusuf Tuggar, da takwaransa na Angola, Tete António, sun rattaba hannu kan yarjejeniyar a madadin ƙasashensu. Najeriya da Angola sun

Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Ambasada Yusuf Tuggar, da takwaransa na Angola, Tete António, sun rattaba hannu kan yarjejeniyar a madadin ƙasashensu.

Najeriya da Angola sun rattaba hannu kan yarjejeniyar haɗin gwiwa ta kawar da buƙatar biza ga masu riƙe da fasfo na diflomasiyya da na hukuma.

An sanya hannu kan yarjejeniyar ne a ranar Lahadi, 15 ga Fabrairu, 2026, a gefen zama na 39 na Tarayyar Afirka a Addis Ababa, Habasha.

Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Ambasada Yusuf Tuggar, da takwaransa na Angola, Tete António, sun sanya hannu kan yarjejeniyar a madadin ƙasashensu.

Tuggar ya bayyana cewa wannan yarjejeniya “ta daɗe tana kan hanya kafin ta tabbata.”

Ya ce, “Wannan abu ne mai matuƙar muhimmanci domin zai bai wa jami’an gwamnati damar zirga-zirga tsakanin Najeriya da Angola cikin ’yanci, ba tare da wata tangarda ko tsaiko ba.

“Kuma wannan shi ne ginshiƙin ƙarfafa dangantaka tsakanin Najeriya da Angola. Idan jami’an gwamnati suna zirga-zirga cikin sauƙi, hakan yana samar da damar da ɓangaren masu zaman kansu da sauran jama’a za su ma su yi zirga-zirga cikin sauƙi.

“Don haka fatanmu da addu’armu ita ce, a nan gaba ba da daɗewa ba, ’yan Najeriya da ’yan Angola za su riƙa zirga-zirga tsakanin ƙasashen biyu cikin ’yanci, ba tare da wata tangarda ko tsaiko ba, domin mu ’yan’uwa ne na juna.

“Haka kuma yana da matuƙar muhimmanci cewa ana sanya hannu kan wannan yarjejeniya a nan Addis Ababa.”

Tuggar ya lura cewa duk da cewa wasu matasa ba za su tuna ba, jawabin tarihi da marigayi shugaban ƙasar Najeriya, Murtala Muhammed, ya gabatar ya zama babban juyin juya hali a siyasar Afirka da Angola, kuma an gabatar da shi ne a Addis Ababa shekaru da dama da suka wuce.

Ya ƙara da cewa, “Ina matuƙar farin ciki da cewa muna sanya hannu kan wannan yarjejeniya a nan. Kuma ina da cikakken tabbaci cewa dangantakar za ta ci gaba da ƙara ƙarfi da ƙarfi.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted