Najeriya: A Sakonsa Na Sabuwar Shekara Shugaba Tinubu Ya Sanya Fata A Zukatan Yan Najeriya, Ya Kuma Amince Da Tsadar Rayuwa

Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu, a sakonsa na sabuwar shekara ta 2025 wanda aka watsa a ranar Laraba, ya bayyana cewa ya fahinci irin

Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu, a sakonsa na sabuwar shekara ta 2025 wanda aka watsa a ranar Laraba, ya bayyana cewa ya fahinci irin matsalolin da  mafi yawan yan kasarsa suka fuskanta a shekarar ta 2024, amma ya ce akwai fatan mai yawa a cikin sabuwar shekara ta 2025 sauki na kan hanya.

Jaridar Premium times ta Najeriya ta nakalto shugaban yana lissafa irin ci gaban da gwamnatinsa ta samu a shekarar da ta gabata ta 2024, sannan ya amince da cewa yan Najeriya sun sha wahaka sosai musamman dangane da tsadar Abinci da magunguna, ya kuma kara da cewa hakan ya faru ne tsarinsa na tafiyar ta kasar.

A wani wuri a jawabinsa shugaban ya ce farashin man fetur ya na zuwa kasa-kasa a hankali, haka ma darajar Naira ya na kara karfi saboda yawan ajiyar da gwamnatinsa take da su a kasashen waje.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments