Masu zanga-zanga a duk fadin siriya sun bayyana rashin amincewarsu da ci gaba da kisan mabiya mazhabar Aalawiyya a bakin nruwan tekun medeteranin. Da kuma rikicn da ya kai ga zubar da jnin mutanen kasar a Sewaida saboda shishigin da HKI take yi a cikin al-amuran cikin gida na kasar.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kafafen yada labaran kasar suna fadar cewam dubban mutanene suka fito suka kuma taru a babban dandalin da ke tsakaiyar suwaida inda suke kira ga gwamnatin rikon kwarya ta HTS ta janye yan ta’addan da ta tura zuwa yankin suwaida don kashe mutanen yankin.
Masu zanga zangar suna dauke da alluna wadanda aka rubuta a kansa : a bude hanyoyi don shigo da abinci zuwa yankin Suwaida. Masu zanga zangar sun bayyana cewa mayakan HTS sun toshe hanyoyin shgiga yankinn Suwaida wanda ya hana abinci shigowa lardin tun watan da ya gabata.
Masu zanga-zangar sun bayyana cewa basa sun gwamnatin Shaar ta gudanar da bincike a cikin al-amarin da take da hannu a cikinsa.