Mutane Biyu Ne HKI Ta Kashe A Wani Harin da Ta Kai Kan Wani Cocin Catholica A Gaza

A wani harin da jiragen yakin HKI suka kai kan cocin Holy Family a cikin birnin Gaza yayi sanadiyyar mutuwar Falasdinawa biyu sannan wasu da

A wani harin da jiragen yakin HKI suka kai kan cocin Holy Family a cikin birnin Gaza yayi sanadiyyar mutuwar Falasdinawa biyu sannan wasu da dama suka ji rauni.

Labarin ya kara da cewa paparoma Leo na 16 ya bayyana damuwarsa da wadannan hare-hare ya kuma bukaci a tsagaita budewa juna wuta a jiya 17 ga watan Julai.

Har’ila yau Cardinal Pierbatista Pizzaballa, na birnin Qudus wanda kuma yake kula da cocin na Gaza ya tabbatar da hare-haren, ya kuma kara da cewa tankar yaki na HKI ce ta budewa cocin wuta, sannan ya bayyana mutane biyu da suka rasa rayukansu masu sunaye Saad Issa Kostandi Salameh da kuma Foumia Issa Latif Ayyad.

Ya kara da cewa wannan shi ne coci guda na mazahabar catholica da ke Gaza, kuma tsirarun cristocin da ke yankin gaza suna daukarsa a matsayin wurin fakewa daga makaman HKI.

Labarin ya kara da cewa wannan bas hi ne karon farko da kai hare-hari a kan cocin ba wani sojan HKI ya kashe mata biyu a shekara ta 2023 wadanda suke samun mafaka a cocin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted