Ma’aikatar sufurin kasar Kazakhstan ta sanar da cewa a yau Laraba wani jirgin jigilar matafiya mallakin kasar Azerbaijan tare da kashe mutane 67 da kuma matuka da ma’aikatansa. Sai dai wasu mutane 25 sun tsira da rayukansu.
Jirgin dai yana kan hanyarsa ne daga Baku zuwa Grozni na kasar Rasha.
Kamfanin dillancin labarun “Interfax” ya ce; mahukuntan kasar ta Kazakhstan sun fara binciken musabbabin faduwar jirgin.