Najeriya: Yarjejeniyar Zaman Lafiya Tsakanin Musulmi Da Kirista

shuwagabanin kungyoyin musulmi da kristoci sun jagoranci taron zaman lafiya

Fiye da jagororin addinin musulunci da na Kiristoci 50 ne suka jagoranci sa hannu a wata yarjejeniyar zaman lafiya a Abuja, bayan da suka kaddamar da wata tafiya da zata samar da zaman lafiya ba tare da banbance-banbancen addini ba da nufin ciyar da kasar gaba  da kuma shawo kan matsalolin da ake fuskanta.

Sakataren Majalisar koli ta addinin Musulunci Mohammad Al-Issa ya ce zaman taron cikakkiyar dama ce ga mabiya addinan biyu sun sauya tarihi a kasar, wajen rungumar zaman lafiya tare da watsi da banbance-banbancen da ke tsakaninsu.

A gefe guda John Praise Daniel, shugaban kungiyar Kiristocin Najeriyar reshen arewaci, ya yi fatan malamai da limaman dukkanin addinan da suka halarci taron su yi aiki da matsayar da aka cimma wajen samar da zaman lafiya tsakanin al’umma.

Shi ma Sakatare Janar na kungiyar Jama’atu Nasril Islam ya ce matsayarsu a taron bata nufin kowanne bangare ya bar addininsa, sai dai fatan da ake da shi shi ne ayi aiki tare don samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted