Isra’ila Ta Kwace Gidajen Falasdinawa A Yammacin Kogin Jodan

sojojin isra'ila sun kwacewa wasu falasdinawa gidjensu a gabar yammacin kogin jodan

Rahotanni sun bayyana cewa sojojin isra’ila sun kwace gidjen wasu falsdinawa a kuyen Qusra kwanaki bayan kwace kauyen dake gabar yammacin kogin Jodan, kuma sun kwace gidagen falasdinawa guda 8 a kauyen qusra a garin Nablus dake yankin falasdinu a jiya alhamis

Sojojin Isra’ila sun fara kwace yankin na Qusra ne tun a ranar lahadi inda sojojin Isra’ila da wasu yahudawa yan share wuri zauna sun kafa tenti inda suka rufe kofar shiga wasu gidaje guda 3 dake saman kauyen, kuma suna hana ruwa da wutar lantarki da kuma motar Asibiti isa wajen don daukar wani yaro mara lafiya.

Ministan harkokin wajen  yankin falasdinu ya fitar da wani bayani inda yayi tir da yahudawa yan gudun hijira  da suka kai hare-hare da ake bayyanashi a matsayin na ta’addanci, ya kuma ce gwamnatin tel aviv tana amfani da yan gudun hijira a matsayin kayan aiki don cimma manufofinta da kuma mamaye yammacin kogin jodan

Tun daga lokacin sojojin Isra’ila da sauran yahudawa yan share wuri zauna sun kashe falasdinawa akalla 1182 a fadin yakin gabar yammacin kogin Jodan kuma sun jikkata dubbai da kuma tilastawa mutane 24000 tserewa daga gidajensu ba shiri.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted