Ministan harkokin wajen kasar iran Abbas Araqchi ya bayyanawa takwarorinsa na kasashen Girka da Austeriya cewa kungiyar tarayyar turai ba ta da kyakkyawar dabi’ar da zata iya yi wa kasar Iran Magana kan abin da ya shafi hakkin bil adama idan aka yi laakari da dabi’a mai harshen damo da gwamnatocin kasashen turai ke yi kan laifukan da gwamnatin isra’ila ke tafakawa a yankin
Araqchi yayi wannan bayanin ne a tattaunawa ta wayar tarho da suka yi da ministan harkokin wajen girka giogo gerapetritis da kuma na Austriya beate mainl resinger a jiya Alhamis inda ya caccaki kungiyar tarayyar turai game da munafunci da take nunawa kan kare hakkin dan Adam,
Haka zalika Araqchi yayi watsi da bayanan da kungiyar EU ta fitar na take hakkin dan adam a kasar Iran , yace duk da ayyukan da tace tana yi a bangaren kare hakkin dan Adam, amma ba ta da kyawawan halayen da za ta iya yi wa wasu huduba kan kare hakkin dan adam
Yace siyasar kungiyar tarayyar Turai ta taimaka sosai wajen ci gaba da mamayar da isra’ila ke yi da kisan kare dangi da take yi wa falasdinawa don haka yayi kira ga kasashen turai da su lura da irin yadda suke tunkarar alumma don samun ci gaba a yammacin asiya.