Jakadan kasar Iran kuma mataimakin wakilin Iran na din din din a majalisar dinkin duniya yayi watsi da zargin da kasar Amurka ta yi mata mara tushe inda ta ce tana amafani da jiragen sama na yan kasuwa wajen yin jigalar makamai da sauran kayayyakin soji zuwa kasar Yamen
A cikin wata wasika da ya aikewa shugaban majalisar dinkin duniya Antonio Guterres da kuma shugaban kwamitin tsaro na majalsar dinkin duniya inda yayi watsi da wadannan zarge-zarge da wakilin Amurka ya gabatar da kuma wasu mambobi a kwamitin tsaro na majalisar dinkin lokacin da ake zama kan kasar Yamen
Haka zalika yace zargin ba shi da tushe balle madogara da babu wata hujja mai karfi da zaa yi amfani da ita akai, kuma ya zargi Washington da kokarin karkatar da akalar kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya, kuma ya bayyana matakin a matsayin munafinci da kasar Amurka take yi don kawar da hankali game da abin da take tafkawa a kasar Yamen da suran yankin baki daya .
Idan ana iya tunawa matakin soji da kasar Amurka ta dauka kan kasar yamen a watan maris din shekara ta 2025 ta keta hurumin kasar da martabarta kuma yayi hannun riga da kudurin majalisar dikin duniya da ma na kwamitin tsaro na MDD