A jiya Asabar ce rikici ya barke tsakanin jami’an tsaro na kan iyakar kasashen Afgistan da Pakistan wanda ya kai ga rasa rayuwa na Jami’an tsaro a bangarorin biyu da kuma wasu fararen hula.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa rikicin ya auku ne a garuruwan Khost – Paktia na kan iyakar kasashen biyu daga yamma.
Labarin ya kara da cewa jami’an tsaron Pakistan 19 ne suka mutu a yayinda fararen hula 3 suka mutu a bangaren kasar Afganistan, wannan banda wadanda suka jikata.
Kamfanin dillancin labaran ‘Tolo” na kasar Afganistan ya ce sojojin kasar Pakistan ne suka fara bude wuta a kan wadannan yakuna a Afganistan, sannan jami’an tsaro na Afganistan suka maida martani.
Har’ila yau kafafen yada labarai na kasar Pakistan sun bayyana cewa a safiyar yau Lahadi ma, an sami rahoton musayar wuta tsakanin jami’an tsaro na kan iyakar kasashen biyu. Inda a nan ma aka kashe mutane da dama a bangarorin biyu, sannan wasu suka ji rauni.
Tun bayan da kungiyar Taliban da sake komawa kan ragamar iko a kasar Afganistan a shekara ta 2021 ne, aka fara rikice-rikice a kan iyakar kasashen biyu. Wadanda suka hada da kungiyoyi masu kishin addini da kuma rikicin kabilanci da bambancin ikida.