Wani mummunan hatsari ya afku a Masar inda ‘yan mata 18 suka mutu sakamakon fashewar wata motar dakon mai
Wani mummunan hatsarin mota ya afku a kasar Masar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar wasu mata 18 da direban bas a kan hanyarsu ta zuwa gonar inabin domin girbin inabin.
Hatsarin ya afku ne a ranar Juma’a a kan hanyar yankin da ke gundumar Menoufia, bayan wata babbar mota ta yi karo da motar bas din da ke dauke da ‘yan matan 18. Dukkansu sun fito ne daga kauye daya, Kafr El-Sanabseh, a gundumar Menoufia, kuma dukkansu ‘yan kasa da shekara 21 ne.
Hotunan wannan mummunan hatsarin da aka yi ta yawo da su a shafukan sada zumunta, sun nuna yadda motar bas din ta lalace gaba daya. Hotunan akwatunan gawarwakin ‘yan matan da aka jera su sun haifar da bakin ciki sosa a tsakanin al’umma.
Jami’an tsaro sun cafke direban babbar motar da ke da alhakin hatsarin bayan ya arce daga wurin. An mika shi ga ofishin gabatar da kara na gwamnati, wanda ke gudanar da bincike.