Search
Close this search box.

Mujallar Amurka Ta Ce Kungiyar Hamas Ce Ta Yi Nasara A Halin Yanzu A Yakin Zirin Gaza  

Mujallar Foreign Affairs ta kasar Amurka ta bayyana cewa: Kungiyar Hamas ta yi nasara a Gaza kuma tana iya kai hare-hare kan haramtacciyar kasar Isra’ila

Mujallar Foreign Affairs ta kasar Amurka ta bayyana cewa: Kungiyar Hamas ta yi nasara a Gaza kuma tana iya kai hare-hare kan haramtacciyar kasar Isra’ila

Mujallar Foreign Affairs ta Amurka a yau Juma’a ta tabbatar da cewa: Kungiyar Hamas ta yi ƙarfi fiye da yadda take a ranar 7 ga watan Oktoban shekara ta 2023, kuma batun Falasɗinawa ya zama mafi shahara kuma mai ban sha’awa a duniya.

Mujallar ta ce a cikin wani rahoto da ta fitar cewa: Bayan watanni tara da fara kai hare-haren haramtacciyar kasar Isra’ila kan Zirin Gaza, ba a samu nasara kan kungiyar Hamas ba, kuma babu alamun samun nasara kanta nan kusa kadan.

Mujallar ta kuma kara da cewa: Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta mamaye Zirin Gaza da sojoji kusan 40,000, tare da tilastawa kashi 80% na al’ummar Falasdinu gudun hijira, tare da kashe Falasdinawa sama da 37,000, tare da jefa bama-bamai akalla tan 70,000 a yankin, gami da lalata fiye da rabin gine-ginen yankin da kuma hana ruwa da abinci da wutar lantarki a yankin, lamarin da ya wurga daukacin al’ummar yankin cikin masifar yunwa.

Duk da cewa, masu lura da al’amura da dama sun bayyana rashin dan adamtakar yahudawan sahayoniyya da mummunar dabi’ar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila, amma a kullum shugabannin haramtacciyar kasar ta Isra’ila suna yin ikrarin cewa sun yi kusan kawo karshen kungiyar Hamas da raunana karfinta, amma abin da ya bayyana a fili shi ne cewa: Ikon kungiyar Hamas na karuwa sosai fiye da yadda ake tsammani.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments