Minsitan Harkokin Wajen Iran Ya Tattauna Da Takwaransa Na Yemen Akan Halin Da Ake Ciki A Yammacin Asiya

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Arakci ya tattauna ta wayar tarho da takwaransa na kasar Yemen Jamal Ahmad Ali Amiri akan halin da ake

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Arakci ya tattauna ta wayar tarho da takwaransa na kasar Yemen Jamal Ahmad Ali Amiri akan halin da ake ciki a yammacin Asiya, tare da yin musayar ra’ayi.

Ministan harkokin wajen na Iran ya bayyana tsagaita wutar yaki a Gaza, a matsayin sakamakon tsayin dakar ‘yan gwgawarmaya a Gaza da kuma goyon bayansu da mutanen Yemen su ka yi.

Ministan harkokin wajen na jamhuriyar musulunci ta Iran ya yi ishara da rawar da Yemen ta taka wajen taimaka wa ‘yan gwgawarmaya a Gaza sannan ya kara da cewa: Bayan gushewar watanni 15 na aikata laifuka da kuma kisan kiyashi a Gaza, ‘yan sahayoniya ba su iya cimma daya daga cikin manufofin da su ka shata ba da su ka hada da ganin Falasinawa sun mika kai.

Arakci ya kuma yi ishara da ziyarar bayan nan da dan sakon musamman na babban magatakardar MDD ya kawo Iran, tare da bayyana cewa, ta yi amfani, sannan kuma ya jaddada ci gaba da taimaka wa gwamnati da al’ummar Yemen.

Shi kuwa ministan harkokin wajen Yemen ya bayyana gamsuwarsa da tsagaita wutar yaki a Gaza, sannan ya kara da cewa: Muna bibiyar yadda ake aiwatar da tsagaita wutar yaki.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments