Ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa sun yi gargadi kan sakamakon da ke tattare da kaddamar da gagarumin farmakin Isra’ila kan kasar Labanon bisa la’akari da abubuwan da ke faruwa a baya-bayan nan, wanda zai iya haifar da barkewar yaki a yanki baki daya, da kuma barazana ga tsaro da zaman lafiyar yankin gabas ta tsakiya.
A yayin taron tuntubar juna na shekara – shekara na majalisar kungiyar hadin kan kasashen Larabawa, ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar sun tabbatar da cikakken goyon bayansu ga gwamnati da al’ummar kasar Lebanon, dangane da yadda Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare a Lebanon.
Ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa sun yi kakkausar suka kan yadda Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare kan kasar Labanon.
Har ila yau, sun bayyana cikakken goyon bayansu ga kasar Labanon, wajen tinkarar wannan ta’addanci, tare da dorawa “Isra’ila” dukkan nauyin wannan mummunar ta’addanci, da kuma gargadin sakamakon da ke tatatre da hakan.
Ministocin sun amince da gudanar da zama na hadin gwiwa da kungiyar kasashen musulmi ta OIC a cikin kwanaki masu zuwa, domin isar da sako karara ga kasashen duniya kan bukatar dakatar da yakin Isra’ila cikin gaggawa.
An gudanar da taron tuntuba na shekara shekara na majalisar kungiyar kasashen Larabawa a matakin ministocin harkokin waje a gefen babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 79 a birnin New York.
Harin na Isra’ila kan kasar Labanon, ya yi sanadiyyar yin shahadar mutane 492, yayin da adadin wadanda suka jikkata ya kai kusan 1,645, kamar dai yadda kididdigar ma’aikatar lafiya ta kasar Lebanon ta tabbatar.
Ma’aikatar ta bayyana cewa harin da Isra’ila ta kai ya yi sanadiyar mutuwar kananan yara 35 da mata 58.