Ministan tsaron kasar Iran ya yi kira da a dauki kwararan matakan ladabtarwa kan Amurka da gwamnatin ‘yan sahayoniyya
Ministan tsaron kasar Iran Birgediya Janar Aziz Nasirzadeh, a wata tattaunawa ta wayar tarho da takwararsa ta kasar Afirka ta Kudu, Angie Motshekga, ya jaddada cewa; lokaci ya yi da kasashe masu cin gashin kansu irin su Iran, da Afirka ta Kudu, da sauran mambobin kungiyar BRICS, za su dauki kwararan matakai masu inganci kan munanan manufofin Amurka da gwamnatin ‘yan sahayoniyya.
A cikin ganawarsu ta hanyar wayar tarho, bangarorin biyu sun jaddada karfafa hadin gwiwar kasa da kasa da fuskantar fandararru da goyon bayan hadin kan kasa da kasa.
Birgediya Janar Nasirzadeh ya yaba da matsayin kasar Afirka ta Kudu bisa ka’ida da kuma matakan shari’a na goyon bayan al’ummar Falastinu da ake zalunta tare da yin Allah wadai da matakin da gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta dauka kan Iran da Gaza yana mai cewa: “Matsayin gwamnatin Afirka ta Kudu ya samo asali ne daga ruhin adalci da nuna kyama ga mummunar dabi’ar nuna wariyar launin fata da al’ummar wannan kasa ta dandana.”
Yayin da yake ishara da harin wuce gona da irin da yahudawan sahayoniyya suka kaddamar kan kasar Iran a baya-bayan nan, ministan tsaron kasar Iran ya bayyana cewa: Harin da aka kai kan wuraren zaman fararen hula da cibiyoyi ya kasance keta dokokin kasa da kasa ne karara. Kuma ta mayar da martani da kakkausan harshe, kamar yadda yahudawan sahayoniyya suka yi kira da a tsagaita bude wuta ta hanyar shiga tsakani da kuma bukatar Amurka. Al’ummar Iran ta amince da bukatarsu ta hana yaduwar rikici da ci gaba da rurutarsa, amma a shirye Iran take ta mayar da martani a kodayaushe.