Ministan Tsaron Iran Ya Ce: Sun Gudanar Da Gwajin Sabbin Makamai Masu Linzami

Ministan Tsaron kasar Iran ya bayyana cewa: Sun gudanar da gwajin sabbin makamai masu linzami Ministan tsaron kasar Iran Birgediya Janar Aziz Nasirzadeh ya bayyana

Ministan Tsaron kasar Iran ya bayyana cewa: Sun gudanar da gwajin sabbin makamai masu linzami

Ministan tsaron kasar Iran Birgediya Janar Aziz Nasirzadeh ya bayyana cewa: A cikin shekarar da ta gabata, an gwada sabbin makamai masu linzami da ke dauke da manyan kawuna na yaki da karfin tuwo, lamarin da ya ba su damar kutsawa cikin tsarin tsaron sararin samaniyar abokan gaba. A wata hira da gidan talabijin na kasar Iran a yammacin jiya Juma’a, yayin da yake ishara da ma’auni na yakin baya-bayan nan da kuma sabbin barazanar da ake yi wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Birgediya Janar Nasirzadeh ya ce: Wannan yakin da aka dora wa Iran na baya-bayan nan ya gabatarwa kasar fage da suka nuna al’ummar Iran wuraren da ya zama wajibi su gudanar da ayyukansu na kai farmaki da wanzar da tsaro. Ya kuma jaddada cewa dole ne a tsara makomar masana’antar tsaron kasar bisa irin wadannan abubuwa da kuma tsari.

Dangane da kwatanta irin karfin kariya da Iran take da shi da makiya a yakin kwanaki 12, ya ce: Iran ba ta fuskanci wata barazana ta yau da kullun ba a wannan yakin, a maimakon haka, mafi karfin soji a duniya ne ya haddasa wannan lamarin, bai kamata a yi la’akari da cewa gwamnatin ‘yan sahayoniyya ita kadai ce a kan Iran ba, a maimakon haka, Amurka da wasu kasashen Turai da na yammacin Turai su ma sun shiga yakin ta fuskar gabatar da kayan aiki, tallafi da kwararru ga ‘yan sahayoniyya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments