Ministan leken asirin kasar Iran Hujjatul-Islam Seyyed Isma’il Khatib ya bayyana cewa: Tasirin Iran ya kasance a kodayaushe, kamar yadda take da tasiri a sauran kasashe ciki har da na ‘yan sahayoniyya.
A yayin tattaunawa game da nasarorin da ma’aikatar leken asiri ta kasar Iran ta samu, Hujjatul-Islam Seyyed Ismail Khatib ya ce, “Tasirin yana wanzuwa a kodayaushe, kamar yadda suke da tasiri a sauran kasashe ciki har da haramtacciyar kasar ‘yan sahayoniyya.”
Ya kara da cewa: “Kowane irin tasirin da ake da shi, bangaren shari’a zai sanar da shi, duk wani matakin wuce gona da iri da za a dauka a kan sojojin Iran da dakarun kare juyin juya halin Musulunci (IRGC), da ma’aikatar leken asiri, da kuma hukumar leken asiri ta IRGC, hukumar shari’a ce zata yi hukunci kansa. Abin da aka sanar a cikin kafafen watsa labarai da bayanai an riga an shige wannan fagen ne, ba wai abin da za a iya zato ba ne, ko kuma abin da aka samu ta hanyar da ba gaskiya ba.”
Da yake amsa tambaya kan ko ma’aikatar leken asirin ta bayyana wani abu kawo yanzu wajen gano gibin da ke tattare da tasirinta?, ministan ya nuna cewa “za a bayyana nasarorin da aka samu nan gaba”.