Ministan Tsaro Na Riko na kasar Iran ya ce sojojin kasar suna dauke da abubuwan mamaki ga makiya nan gaba.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Janar Majid Ebn Reza yana fadar haka a yau Jumma’a ya kuma kara da cewa, ilmin da Iraniyawa suke da shi, da abinda matasan kasar suke da su da kuma abubuwan da suke faruwa a masana’antun makaman kasar abubuwan ban mamaki ne ga masoya ballanta makiya, da yardar All…
A wani labara ministan ya bayyana a jiya Alhamis kan cewa Iran ta sauya al-amura a yankin yammacin Asia ta hanyar bayyana karfinta ga makiya a fagen fama wanda ya nuna cewa, zamanin sari ko noke kuma ya wuce, ko jigilar sojojin daga teku zuwa teku da kuma barazanar yaki duk sun wuce.
Janar Ibn Reza ya kammala da cewa, abubuwan da ake nunawa a kafafen yada labarai na makiya ba zai canza abinda yake faruwa a kasa ba, ko kuma ba zai tabbatar da nasara ga wanda ya sami nasara ko ya fadi a yaki ba.
Daga karshe ya bukaci makiyan kasar su karanta tarihin kasar Iran na dubban shekarun da suka gabata don sanin cewa Iraniyawa suna nan kamar yanda suke a da. Su kuma san yanda zasu yi magana da su.