Ministan makamashin na Iran Jawad Owle ya fada wa manema labaru cewa; Yawan man fetur din da Iran take fitarwa zuwa kasuwannin duniya ya karu daga ganga miliyan 2.2 zuwa ganga miliyan 3.6 a kowace rana.
Ministan ya kuma kara da cewa; Kowace ganga 100 da Iran din take fitarwa, tana ba ta kudin shiga da su ka kai Dalar Amurka biliyan 2.8 a kowace shekara.
Bugu da kari ministan makamashin na Iran ya ce; gabanin karshen wannan shekara ta Iraniyawa, ana shirin ganin cewa a kowace rana an fitar da ganga miliyan 4 a kowace rana.
Ministan makamashin na Iran ya yaba wa kwararru na cikin gida wadanda su ka taka rawa wajen ganin ann sami wannan cin gaban, a fagen bunkasa harkokin man fetur din da ake kai wa kasuwannin duniya.