Ministan kiwon lafiya na Iran Muhammad Ridha Zafarkandi ne ya bayyana cewa, kasar ta Iran ce ta farko a fagen gabatar da nazarce-nazarce da su ka shafi fagen kiwon lafiya mai alakan da ka’idojin ingantattun halaye na likitanci.
Ministan wanda ya gabatar da jawabi a wurin taron karawa juna sani karo na 11 da aka yi a nan Iran dangane da ka’idojin ingantattun halaye na aikin likita ya kara da cewa, an tsara wadannan ingantattun halayen na aikin likita akan yadda za a aiwatar da su a aikace. Haka nan kuma ana koyar da su ga daliban aikin likita a matsayin ka’idar da ake mu’amala ta ‘yan’adamtaka da marasa lafiya.
Bugu da kari ministan kiwon lafiyar na Iran ya ce, yadda ma’aikatan kiwon lafiya za su yi mu’amala da mara lafiya cikin tausayawa da kuma nuna damuwa da matsalar da take damunsa, suna da tasiri matuka.
Ministan kiwon lafiyar ya yi ishara da likitan da zai zama yana kula da iyalai tare da bibiyar tarihin rashin lafiyarsu da kuma nau’in maganin da suke sha, wanda yana a mastayin ginshiki ingantacciyar halayya ta aikin likitanci.