Ministan Harkokin Wajen Rasha Ya Fara Ziyarar Aiki A Nahiyar Afirka

Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov ya fara ziyarar aiki a cikin kasashen nahiyar Afirka tare da yada Zangon farko a birnin Addis Ababa

Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov ya fara ziyarar aiki a cikin kasashen nahiyar Afirka tare da yada Zangon farko a birnin Addis Ababa na kasar HAbasha.

A ganawar da ya yi da shugaban kungiyar tarayyar Afirka ( A.U) Mahmud Ali Yusuf, ministan harkokin wajen kasar ta Rasha ya yi kira ga nahiyar Afirka da ta zama mai taka gagarumar rawa a cikin harkokin kasa da kasa.

 Lavrov ya ce: “Muna goyon bayan abinda ka ambata dangane da gaggauta ganin nahiyar ta Afirka tana taka gagarumar rawa a fagen kasa da kasa da ya hada da samun matsuguni a kwamitin tsaro na MDD.”

Haka nan kuma ya ce, da akwai bukatar a yi wa kwamtin tsaron kwaskwarima domin a fadada shi ta shigar da wakilan kasashen nahiyoyin Asiya,Afirka da kuma yankin Latin.”

Ministan harkokin wajen na Rasha ya kuma yi Ishara da yadda har yanzu tsofaffin ‘yan mulkin mallaka suke ci gaba da wawason albarkatun da Allah ya yi wa nahiyar Afirka.

Kafafen watsa labarun Rasha sun ambaci  cewa ministan harkokin wajen nasu zai tattauna da mahukuntan Habasha akan yadda Rasha za ta gina musu cibiyar samar da makamashi ta Nukiliya.

Sai dai kuma kafafen watsa labarun na Rasha ba su ambaci wace kas ace kuma Lavrov zai ziyarta ba, bayan Habasha.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted