ministan harkokin wajen kasar masar Badar Abdel –Ati ya tattauna ta wayar tarho da takwaransa na kasar iran Abbass Araqchi da kuma manzon musamman na kasar Amurka Steve Witkoff, kuma sun yi kira da a sake farfado da tattaunawar diplomasiya tsakanin Washington da Tehran.
wannan yana duba irin muhimmancin kokarin da masu ruwa da tsaki suke yi na ganin an koma batun tattaunawa domin warware takaddamar da ta sarke a yankin.
kasar masar tana so ta zama mai shiga tsakanin ne, kuma ta jaddada muhimmancin amfani da hanyar diplomasiya domin samar da daidaito a yanki da kaucewa afkuwar duk wani tashin hankali da rashin zaman lafiya.
daga karshe abdul ati ya bayyana muhimmancin kara kaimi wajen rage zaman tankiya da cimma yarjejeniyar zaman lafiya, ya ce dole ne a samar da wani yanayi da ya dace don warware matsalar ta hanyar diplomasiya da kulla yarjejniya da za ta taimaka wajen tabbatar da tsaro da tabbaci a yankin.