Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Zai Halarci Taron Kwamitin Tsaro Na MDD Na Musamman Dangane Da Yaki A Gaza

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’il Baghaei ya bayyana cewa ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi zai halarci taron ministocin harkokin waje a kwamitin

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’il Baghaei ya bayyana cewa ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi zai halarci taron ministocin harkokin waje a kwamitin tsaro na MDD a yau Litinin inda ake saran za’a tattauna al-amura da suka shafi yankin Asiya ta kudu musamman dangane da kasar Falasdinu.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto  Esmaeil Baghaei kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya na fadar haka a yau litinin a taronsa da kafafen yada labarai na mako mako.

 Ya kuma kara da cewa, batun ci gaba da kissan kiyashin da HKI take yi a Gaza na daga cikin al-amuran da ministocin za su tattauna a kansa.

Baghaei ya kara da cewa gwamnatin HKI tana ci gaba da kisan kiyashi da rusa gidajen Falasdinawa a kansu kimanin watanni 16 kenan. A gaban idon kasashen duniya, amma ba wanda ya isa ya dakatar da hakan.

Ya ce: Abin kunya ne kasashen duniya su kasa yin wani abu a kan wannan ta’asar, saboda wasu kasashe wadanda suke amfani da kwamitin tsaro na MDD a matsayin mafaka saboda ci gaba da kissan kiyashi a Gaza.

Baghaei ya tabbatar da cewa kasashen duniya sun tabbatar da cewa an aikata kissan kiyashi a Gaza, kuma dole ne a fuskanci wadanda suke aikata kisan. Ya ce ana saran wannan sabon yunkurin zai sa kasashen duniya zasu bukaci a dakatar da wannan kiyan kiyashin da ke faruwa a Gaza ba tare da bata lokaci ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments