Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Ce Bai Ga Wani Abu Da Ya Faru A Kasar Siriya Wanda Bai Tsammani Zai Faru Ba

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya fadawa jaridar Annahar kan cewa ba wani abin mamakin da ya gani a cikin dukkan abubuwan da

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya fadawa jaridar Annahar kan cewa ba wani abin mamakin da ya gani a cikin dukkan abubuwan da suka faru a kasar Siriya bayan faduwar gwamnatin Bashar Al-Asad.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka ga Jaridar Annahar ta kasar Lebanon. Ya kuma kara da cewa, duk da cewa abubuwa da dama sun faru a cikin dan karamin lokaci, amma an kafa asasinsu gaba daya a cikin shekaru 10-12 da suka gabata.

Ministan yace, gwamnatin HKI ta kai hare-hare babu kakkautawa kan ‘shirin tsaron sararin samaniyar kasar Siriya a cikin watanni 14 da suka gabata, don rage karfin sojojin kasar wajen kare sararin samaniyar kasar.

Yace, bayan fara yakin tufanul aksa watanni 14 da suka gabata, Iran ta fadawa gwamnatin kasar Siriya a cikin watan Satumban da ya gabata kan yiyuwar ta fuskanci matsalolin shugabnci a nan gaba. Mun bukaci gwamnatin ta nuna sassaunci ga masu adawa da shugabancin kasar don rage wannan hatsarin.

Ministan ya ce tun lokacinda aka kafa kwamitin Astana ta sulhuntawa, kasarsa ta fara tuntumar da yan adawar kasar Syriya kai tsaye, sannan tana karfafa tattaunawa kasashe uku a kwamitin Astana,  wato Iran, Turkiyya da kuma Rasha.

Daga karshen yace kungiyar Hezbollah, kungiya ce ta siyasa kuma mai gwagwarmaya da makami a yankin, wacce ta taka rawar a zo a gani a bangarorin biyu. Kuma tana ci gaba da hakan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments