Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Ana gudanar da dukkan ayyukan diflomasiyya cikin cikakken hadin kai tare da hukumomin da abin ya shafa, kuma bisa takamaiman umarni da ayyuka. Ya ce: “Ba za su taba yin kasa a gwiwa ba wajen kare hakki da tsaron al’umma, kuma ba za su taba tasirantuwa da kage-kagen yanayi ba, kuma za su yi aiki da karfi da azama wajen tabbatar da muradun al’ummar Iran.”
Wannan dai ya zo ne a wata hira da gidan talabijin na kasar Iran a yammacin jiya Alhamis, inda ministan harkokin wajen kasar Abbas Araqchi ya amsa tambayoyi kan yarjejeniyar da Jamhuriyar Musulunci ta Iran da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA suka cimma a birnin Alkahira, da kuma ci gaban da aka samu a shawarwari da kungiyar Tarayyar Turai Troika dangane da dage takunkumin kan Iran.
Da yake amsa tambaya kan ko yarjejeniyar da kuma bayanan hukumar ta IAEA game da halin da ake ciki da kuma wadatattun kayayyaki a Iran sun ba da damar sake kai hare-hare kan cibiyoyin, ya ce, “A nan, dole ne a bambanta tsakanin batutuwa biyu. Na farko, tattaunawar Iran da kasashen Turai uku, wadanda suka dade suna ci gaba da gudana tsawon lokaci. Wadannan kasashe uku har yanzu suna da’awar amincewa da yarjejeniyar makamashin nukiliyar, amma Iran ta ci gaba da gudanar da tarurrukan da suka gabata tare da su.” Ko a lokacin Yaƙin kwanaki goma sha biyu, kamar yadda za a iya tunawa, Araqchi ya yi balaguro zuwa ƙasashen waje don halartar taro da yawa na duniya. A birnin Geneva ya kuma gana tare da tattaunawa da ministocin harkokin wajen kasashen da kuma Madam Kalas, babbar wakiliyar Tarayyar Turai. An ci gaba da wannan tattaunawa bayan an gama yakin.