Ministan harkokin wajen kasar Iran ya gana da yarima mai jiran gado na kasar Saudiyya a birnin Riyadh
Ministan harkokin wajen Iran Sayyid Abbas Araqchi ya gana da yarima mai jiran gadon Saudiyya Mohammed bin Salman a yammacin jiya Laraba.
Kamfanin dillancin labaran Saudiyya ya watsa rahoton cewa: Ganawar bangarorin biyu ta yi nazari kan alakar da ke tsakanin kasashen biyu, kuma sun fi mayar da hankali ne kan batutuwan da suka shafi yankin Gabas ta Tsakiya da kuma kokarin da suke yi a tsakaninsu.
Kamfanin dillancin labarai na Iran “IRNA” ya bayyana cewa: Bangarorin biyu sun jaddada wajabcin dakatar da yakin Gaza da na Lebanon da kuma hanzarta shigar da kayayyakin jin kai ga ‘yan gudun hijira.
Abbas Araqhchi ya isa birnin Riyadh ne a jiya Laraba a zangonsa na farko na rangadin da ya ke yi a yankin Gabas ta Tsakiya kuma ya samu tarba daga mahukuntan Saudiyya a hukumance.