Ministan Harkokin Wajen Burkina: An samu babban ci gaba na  hadin gwiwa tsakaninmu da Rasha

Ministan harkokin wajen Burkina Faso, Karamoko Jean-Marie Traore, ya yaba da yadda kasar ke ci gaba da samun hadin gwiwa da Rasha, yana mai cewa,

Ministan harkokin wajen Burkina Faso, Karamoko Jean-Marie Traore, ya yaba da yadda kasar ke ci gaba da samun hadin gwiwa da Rasha, yana mai cewa, alakar Burkina Faso da Rasha ta fiye mana alaka da Faransa.

Bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a shekarar 2022, Burkina Faso ta balle daga cikin kasashe masu yin biyayay ga Faransa, inda ta kulla alaka da kuma kawance tare da kasar  Rasha.

A taron Rasha da Afirka da aka yi a birnin Sochi, Traore ya kira Rasha a matsayin “abokiyar da za mu iya samun ci gaba da ita” ya kuma jaddada cewa “babu wani tsoro” wajen ci gaba da kara habbaka wannan dangantaka a dukkanin bangarori, da hakan ya hada da hard a bangaren ayyukan soji.

Traore ya kuma bayyana cewa hadin gwiwa da Rasha “ya fi dacewa da al’ummar Burkina Faso fiye da hadin gwiwar da aka kwashe shekaru masu yawa ana yi tsakaninsu da Faransa, wadda ba ta tsinana musu komai ba.

Bugu da kari, Traore ya yi watsi da irin rahotanni da kafofin yada labarai na kasashen turai suke bayarwa dangane da alakar kasarsa da Rasha, yana mai cewa akwai banbanci matuka, domin kuwa sun samu abokai da suke hulda ta gaskiya babu munafunci da zalunci da danniya, sabanin huldarsu da kasashenn yammacin duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments