Abbas Aragchi Ya Kama Hanyar New York Don Halattar UNGA Na 81

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya kama hanya zuwa birnin NewYork Na kasar Amurka don halattar taron babban zauren MDD na shekara shekara

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya kama hanya zuwa birnin NewYork Na kasar Amurka don halattar taron babban zauren MDD na shekara shekara karo na 81.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran na cewa a kan hanyarsa ta zuwa New York Aragchi zai yada zango a birnin Doha na kasar Qatar inda ake saran zai gana da wasu jami’an gwamnatin kasar dangan da sabbin al-amura da suke faruwa a yankin.

Wannan tafiyar tana zuwa ne a dai dai lokacinda shugaban kasar Amurka Donal Trump yake barazanar zai sake farwa kasar ta Iran da yaki. Kuma mai yuwa a wannan karon yakin zai hada har da wasu kasashen Turai da HKI.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted