Babban malamin Addinin musulunci na kasar Bahrain yayi gargadin cewa miliyoyin mutane ne suke shirye da sadaukar da rayuwarsu don bada kariya ga jagoran juyin musulunci na iran Ayatullah imam Khamna’I a daidai lokacin da Amurka ke barazanar kai hari ga iran da ma jagoran addini na kasar.
Shaikh isa Qasim ya bayyana a jiya talata cewa Ayatullah sayyid Ali Khamna’i shi jagora ne na musamman a duniya wanda ya banbanta da sauran shuwagabannin ta hanyar zurfin ilimi na addini da kuma shugabancin siyasa, kuma shi ne wanda miliyoyin mutane maza da mata a iran suka sadaukar da rayukansu a gareshi kuma suke amfani da umurninsa a matsayin umarni na Addini
har ila yau ya kara da cewa alummar musulmin duniya suna goyon bayan kokarin da yake yi wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro da kuma yan uwantaka tsakanin alumomi na duniya
bayanan suna zuwa ne yan makwanni bayan da shugaban Amurka trump yaci zarafin jagora a wasu bayanai da yayi a hirarraki da aka yi da shi da yan siyasa.
a cikin wani jawabi da jagoran juyin musulunci na iran yayi a ranar 17 ga watan janeru yace iran ta dora alhaki kan trump na taimakawa masu tarzoma yan ta’adda da suka gudanar da zanga-zanga a kasar iran a farkon watan janeru.