Wasu jami’an MDD sunn bayyana cewa, a cikin halin da ake ciki a kudancin kasar Lebanon ba ya yuwa mutane yankin su koma gidajensu.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ba bayyana cewa a yau ne wa’adin kwanaki 60 na ficewar sojojin HKI daga kudancin kasar Lebanon kamar yadda ya zo a cikin yarjeniyar da suka cimma da gwamnatin kasar Lebanon watanni biyu da suka gabata.
A safiyar yau ne sojojin HKI suka kashe mutan akalla 15 sannan wasu kimani 83 suka ji rauni a lokacinda suka yi kokarinn komawa gidajensu da ke kudancin kasar Lebanon wadanda sojojin HKI suke mamaye su.
Wakilin MDD na musamman a kan al-amuran kasar Lebanon Jeanine Hennis-Plasschaertand da kuma shugaban rundunar UNIFEL ta MDD Lt. Gen. Aroldo Lázaro
Sun bayyana cewa a cikin halin da ake ciki a kudancin kasar Lebanon. Sun fada a wani taro da kakafafen yada labarai kan cewa lokaci bai yi ba don komawa garuruwan da suke kudancin kasar Lebanon.
Jami’an na MDD sun bayyana cewa, lokacin da aka ayyana a yarjeniyar tsagaita budewa juna wuta na ficewar hki daga yankin bai yi ba.