MDD : Kwamitin Sulhu ya amince da kudurin Amurka kan rikicin Rasha da Ukrain

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da kudurin da Amurka ta zartas kan rikicin Rasha/Ukrain duk kuwa da kauracewar kasashen Turai kwamitin ya

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da kudurin da Amurka ta zartas kan rikicin Rasha/Ukrain duk kuwa da kauracewar kasashen Turai

kwamitin ya kada kuri’ar amincewa da kudurin na Amurka da nufin kawo karshen rikicin da aka kwashe shekaru uku ana yi tsakanin Ukraine da Rasha.

Kuri’u 10 ne suka amince da kudurin, sabili da haka babu wanda ya ki, ko da yake kasashen Turai biyar a majalisar – Denmark, Faransa, Girka, Birtaniya da Slovenia – sun zabi su kauracewa zaben.

Wannan kudurin dai ya tuna da muhimmin kudurin MDD na wanzar da zaman lafiya da tsaro a duniya, tare da yin kira da a warware takaddama cikin lumana da samar da zaman lafiya mai dorewa tsakanin kasashen biyu.

Kafin nan Shugaban kasar Rasha Vladmir Putin ya bayanna cewa, Turawa za su iya shiga cikin shirin warware rikicin Ukraine, yayin da kungiyar EU ke fargabar cewa za a mayar da ita saniyar ware tun bayan fara tattaunawar kai tsaye tsakanin Moscow da Washington.

“Turawa, amma har da sauran kasashe, suna da hakki kuma suna da damar shiga, Kuma zamu mutunta hakan, ”in ji Vladimir Putin a wata hira da aka yi da shi ta talabijin.

Ya nanata cewa kasashen Turai ne suka yanke alaka da Rasha bayan da ta fara kai hari kan Ukraine shekaru uku da suka gabata, Don haka “Shigowarsu a cikin tsarin tattaunawar ya zama dole.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments