Search
Close this search box.

MDD : Ana Bukatar Samun Cikakkiyar Tsagaita Wuta Domin Agaji Ya Samu Kwarara Zuwa Gaza

MDD, ta bayyana cewa ana bukatar samar da cikakkiyar tsagaita wuta ta dindindin domin samuwar kwararar kayan agajiu zuwa Gaza. Domin agaji ya kwarara zuwa

MDD, ta bayyana cewa ana bukatar samar da cikakkiyar tsagaita wuta ta dindindin domin samuwar kwararar kayan agajiu zuwa Gaza.

Domin agaji ya kwarara zuwa Gaza, akwai bukatar a samar da ‘cikakkiyar tsagaita wuta ta dindindin’ Kamar yadda, Sigrid Kaag, jami’ar kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya a Gaza, ta bayyana wa kwamitin sulhu MDD, kan halin da ake ciki na baya-bayan nan a yankin.

Jami’ar ta ci gaba da cewa ba a kai isashen agajin da ake bukata ya shioga shiga a Gaza ba.

Ms Kaag ta kuma mai da hankali kan bukatar kungiyoyin Majalisar Dinkin Duniya su sami karin “hanyoyi daban-daban da ke shigowa cikin Gaza” kuma ta ce tana tattaunawa da jami’an Isra’ila don yiwuwar sake bude babbar hanyar Rafah, a wani mataki na farfado da yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments