Mayakan Izzuddeen Al-Qassam Sun Halaka Ayarin Sojojin Isra’ila A Wani Harin Kwanton Bauna

‘Yan gwagwarmayar Falasdinawa sun kashe wani gungun sojojin Isra’ila a wani harin kwantan bauna da suka kai kan ayarin sojin na Isra’ila Dakarun Izzuddeen Al-Qassam

‘Yan gwagwarmayar Falasdinawa sun kashe wani gungun sojojin Isra’ila a wani harin kwantan bauna da suka kai kan ayarin sojin na Isra’ila

Dakarun Izzuddeen Al-Qassam bangaren sojin kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas sun sanar da cewa: Mayakansu sun kai farmaki kan ayarin sojojin mamayar Isra’ila bayan da suka yi musu kwanton bauna.

Dakarun Qassam bangaren sojin kungiyar Hamas sun fitar da sanarwar cewa: Mayakansu sun samu nasarar halaka wani ayarin sojojin mamayar Isra’ila baki daya bayan da suka kaddamar da wani mummunan harin kwantan bauna da suka kai kansu, inda da farko suka halaka wani sojan Isra’ila dan sari ka noke, sannan daga baya suka kai hari kan ayarin tare da nasarar halaka dukkanin sojojin da suke wurin.

Dangane da yankin Jabaliya, dakarun gwagwarmayar Falasdinawa sun yi arangama da sojojin mamayar Isra’ila a yankunan Beit Hanoun a yayin wani sabon farmakin kasa da sojojin mamayar suka sanar da fara kai wa kan yankunan birnin na Beit Hanoun.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments