Matasan Sudan sun koma suna goyon bayan sojoji a yakin da ake yi bayan adawar da suka yi da rundunar sojin kasar
Jaridar Le Monde ta kasar Faransa ta bayyana cewa: Masu rajin kare demokradiyya wadanda ke adawa da hambararriyar gwamnatin shugaban kasar Omar Hasan al-Bashir, sannan kuma da Janar-Janar din da suka biyo bayansa, a halin yanzu sun shiga sahun sojojin kasar domin kalubalantar mayakan kungiyar Rapid Support Forces ta Dakarun kaidaukin gaggawa.
Har ila yau, Jaridar ta rubuta labarin Kamal Al-Din Al-Nur, wanda ke zaune a kan rufin wani gini, yana duban yadda bakin hayaki ke tashi sama daga yankunan arewacin birnin Khartoum fadar mulkin kasar, a cikin unguwar da ake kira Khartoum Bahri, yankin da aka haife a ciki, inda ake gwabza fada tsakanin sojojin kasar da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces.