Mataimakin Shugaban Kasar Iran Na Farko Ya Jaddada Wajabcin Damawa Da Kowane Bangare A Fagen Jagorantar Kasar Iran

Mataimakin shugaban kasar Iran na farko ya jaddada cewa; Ra’ayin gwamnati shi ne tattaunawa akan fagen yadda al’amura zasu karfafa Mataimakin shugaban kasar na farko

Mataimakin shugaban kasar Iran na farko ya jaddada cewa; Ra’ayin gwamnati shi ne tattaunawa akan fagen yadda al’amura zasu karfafa

Mataimakin shugaban kasar na farko na kasar Iran Mohammed Reza Aref ya bayyana cewa: Babu wani bambanci tsakanin diflomasiyya da fannin, inda ya ce har yanzu ra’ayin gwamnati shi ne tattaunawa kan hanyoyi kyautata gudanar da madafun iko.

A yayin ganawarsa da malaman jami’ar Shariff ta fasahar kere-kere, Aref ya yaba da irin rawar da al’ummar Iran suka taka a yakin kwanaki 12 da yahudawan sahayoniyya da Amurka suka dorawa Iran, inda ya ce: Matsayin al’ummar Iran da kasancewarsu a fagen kare kasar ya kasance mai karfi wajen yakar makiya, saboda dabarun makiya shi ne cewa bayan harin da aka kai wa bangaren soja na Iran, al’ummar Iran za su dauki matakan yaki da gwamnati Jamhuriyar Musulunci amma sai al’umma suka dauki matakin wargaza makircin makiya ta hanyar jaddada goyon bayansu ga tsarin Jamhuriyar Musulunci.

Ya kara da cewa: A halin yanzu Iran tana da kyakkyawar damar bunkasa kimiyya ta fannin fasahar kere-kere da tsaro ta yanar gizo, kuma an kafa kwamitin bayani don tabbatar da yadda ya kamata a raba aiki tsakanin bangarorin gwamnati da masu zaman kansu, musamman jami’o’i ciki har da Jami’ar Fasaha ta Sharif.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted