Mataimakin shugaban kasar Iran na farko ya bayyana cewa: Iran ta yi nasara ta hanyar soja, zamantakewa da tattalin arziki a yakin kwanaki 12 da ya gabata
Mataimakin shugaban kasar na farko Muhammad Reza Aref ya ce, Sun rasa fitattun mutane da kuma manyan malamai a yakin kwanaki 12 da gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta kakabawa Iran, amma sun yi nasara a fagen soji da zamantakewa da tattalin arziki a lokacin wannan yakin.
Aref ya ce: dabarar Iran ita ce gudanar da shawarwari, kuma sun zo kan ingantacciyar dabara kuma sun yi aiki bisa tsarin manufofi da umarnin Jagoran juyin juya halin Musulunci dangane da hakan.
Ya kara da cewa: “An dora musu yakin ne a lokacin da suke tattaunawa da Amurka, kuma a fili yake cewa makiya sun yi niyyar hambarar da gwamnatin kasar Iran da tunanin kawar da ita.”
Ya ci gaba da cewa: Makiya sun mayar da shirin makamashin nukiliyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran aikin siyasa ne.
Haka nan kuma ya yi ishara da zaben shugabannin sojojin kasar bayan cin zarafin da gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta yi wa kasar Iran, yana mai cewa: Zaben shugaba a kowace runduna yana daukar makonni, amma a yayin wannan yakin da aka sanya a gaba, bangaren tsaron kasar ya ci gaba da gudanar da ayyukansa kamar yadda aka yi a baya bayan da aka rasa shugabanninsu.