Mataimakin Shugaban Kasar Iran, Javad Zarif Ya Fara Tattaunawa Da Jami’an Diblomasiyya A Gefen Taron Davos

Mataimakin shugaban kasa kan al-amura na musamman Muhammad Javad Zareef ya gana da jami’am diblomasiyya na wasu kasashe a rana ta farko na taron ‘World

Mataimakin shugaban kasa kan al-amura na musamman Muhammad Javad Zareef ya gana da jami’am diblomasiyya na wasu kasashe a rana ta farko na taron ‘World Economic Forum” ko taron tattalin arziki na duniya dake guda na a birnin Davos na kasar Swizland.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya bayyana cewa Zareef ya gana da Abdullateef Rasheed shugaban kasar Iraki a safiyar yau Talata,  inda suka tattauna kan al-amuran da suka shafi kasashen biyu.

Abdullateef ya yi magana dangane da hulda mai tsawo dake tsakanin kasashen IRNA da Iraki. Sannan ya bukaci karin hadin kai tsakanin kasashen biyu. Da kuma aiwatar da ayyukan hadin guiwa tsakaninsu.

Har’ila yau sun yi magana dangane sauye-sauyen da suke faruwa a yankin, da kuma abubuwan da suke barazana da tsaron kasashen yankin Asiya ta kudu. Hakama a bangaren kasa da kasa jami’an gwamnatocin kasashen biyu sun bukaci tabbatar da zaman lafiya a kasashen Falasdinu. Lebanon da kuma Siriya.

Har’ila yau Zareef ya gana da ministan harkokin wajen Norway Span Borethaid inda suka yi magana kan sauye-sauyen da suke da ke faruwa a yammacin Asiya. Zareef ya godewa kasar Norway kan mutunta sammacin kama Natanyahu da kum yin allawadai da HKI. Zareef ya gana da shugaban kasar Sabiya, kungiyar kasuwanci ta duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments