Mataimaki kwamandan dakarun juyin juya halin Musulunci ya jaddada cewa: Ba za su yi watsi da Amurka da ‘yan sahayoniyya koda na wani lokaci guda ba
Mataimakin kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Birgediya Janar Ali Fadavi ya bayyana cewa: Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na IRGC ba za su yi watsi da manyan makiyansu wato Amurka da ‘yan sahayoniyya ba koda na wani dan lokaci.
Birgediya Janar Fadavi ya bayyana a yau Litinin a wajen bikin karrama tsohon kwamandan dakarun Ansarul- al-Mahdi (AS) da kuma dakarun ta 36 a lardin Zanjan (arewa maso yamma), tare da gabatar da sabbin kwamandojin nasu: Kiyayyar girman kan duniya kan Iran ya fara ne tun daga farkon nasaran juyin juya halin Musulunci, kuma bai daina ba har zuwa yanzu.
Ya kara da cewa: Wadannan hare-haren makirce-makirce kan Iran sun kara tsananta tun bayan nasarar juyin juya halin Musulunci, to amma al’ummar Iran ta hanyar gudanar da ayyukan Ubangiji suna dagewa tare da alfahari.
Yayin da yake ishara da dabarun Imam Khumaini (RA) mataimakin kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Imam (RA) ya kasance yana jaddada cewa wajibi ne a sauke nauyin da ya rataya a wuyanmu, ba wai don cimma sakamako ba, sakamakonsa yana hannun Allah, don haka aikin al’umma shi ne yin abin da ya doru a kan al’umma.