Search
Close this search box.

Masu Gwagwarmaya A Iraki Sun Cilla Makamai Masu Linzami Kan Tuddan Golan Na Kasar Siriya Da Aka Mamaye

Dakarun kungiyoyin musulmi masu gwagwarmaya a kasar Iraki sun bayyana cewa sun cilla makamai masu linzami kan tuddanb Golan na kasar Siriya wanda HKI take

Dakarun kungiyoyin musulmi masu gwagwarmaya a kasar Iraki sun bayyana cewa sun cilla makamai masu linzami kan tuddanb Golan na kasar Siriya wanda HKI take mamaye da su.

Gamayyar kungyoyi masu gwagwarmaya day an ta’adda a kasar Iraki sun bayyana cewa sun yi amfani da makaman Drones ko jiragen sama wadanda ake sarrafasu daga nesa samfurin ‘Kamikaze’  masu kunan bakin wake a jiya Litinin.

Kafin haka dai HKI ta mamaye wadannan yankuna na kasar Sioriya ne a yakin shekara 1967 tsakaninta da wasu kasashen larabawa daga ciki hard a kasar Siriya.

Sanarwan da gamayyar kungiyoyin suka fitar ta kara da  cewa sun aiwatar da wadannan hare haren ne saboda tallafi ga Falasdinawa wadanda suke fafatawa da HKI a gaza ton ranar 7 ga watan octoban shekarar da tga gabata.

Gamayyar kungiyoyin dai sun sha kai irin wadannan hare hare kan wurare daban daban na kasar Falasdinu da aka mamaye.

Ya zuwa yanzu dai sojojin HKI sun kashe Falasdinawa kimani 40,000 a yaynda wasi kimani 80,000.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments