Masar ta sake bude ofishin jakadancinta a Tripoli, babban birnin kasar Libya, na farko bayan shekara 12.
An rufe ofishin jakadancin tun shekarar 2014, lokacin da tashin hankali ya mamaye kasar.
Ministan harkokin wajen Masar Badr Abdelatty ya bude ginin ofishin jakadancin a Tripoli bayan ya isa Libya a ranar Asabar.
Gwamnatin Tripoli ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa sake bude ofishin alama ce ta ci gaban ”dangantakar kasashen biyu.”
Akwai ayyuka masu kyau, ciki har da gina bututun iskar gas da ke hada Libya da Masar, ganin cewa Masar ita ce kadai kasa a Gabashin Bahar Rum,” in ji Ministan Harkokin Wajen Masar Badr Abdelatty.
Sake bude ofishin jakadancin ya zo ne makonni bayan da majalisar dokokin Libya, wacce ke gabashin kasar, ta amince da yarjejeniyar teku da aka dade ana takaddama a kai da Turkiyya, lamarin da ya haifar da fushi na Alkahira, wadda ta ce yarjejeniyar ta mamaye yankin ruwanta.
Kasar Libya dai ta soma farfadowa daga rudanin da ya biyo bayan matakin kasashen NATO na marawa boren 2011 wanda ya yi awan gaba da mulkin tsohon shugaban kasar Muammar Gaddafi.
A halin yanzu Libya na fama da mulkin Gwamnatoci guda biyu ta Tripoli wadda Majalisar Dinkin Duniya ta amince da ita, karkashin jagorancin Firaminista Abdulhamid Dbeibah, da kuma abokin hamayyarsa a gabas, karkashin Khalifa Haftar. Masar ta kasance mai goyon bayan Haftar a gabashin Libya.