Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sanya hannu kan yarjeniyar kiwon lafiya da gwamnatin Amurka wanda zai lakume dalar Amurka biliyon $5Bn.
Jaridar Dily Trust ta Najeriya ta nakalto cewa yarjeniyar tana bukatar Najeriya a bangarenta zata mika dukkan bayanin marasa lafiya wadanda suka amfana da shirin ga gwamnatin Amurka. Kuma ko da nan gaba gwamnatin Najeriya ta dauki shawarar kawo karshen aiki da yarjeniyar bayanan yan Najeriya da ta mikawa Amurka ba zai sake komawa hannunta ba.
Kafin haka dai gwamnatin kasar Ghana ta ki amincea da tayin Amurka na aiki tare kan irin wannan tsari na kiwon lafiya da Amurkan kan mutanen kasarta.
Shugaban kasar Ghana Mahama ya bayyana a ranar 25 ga watan Satumba a birnin NewYork inda ya halarci taron babban zauren MDD karo na 81 kan cewa Amurka ta gabatarwa kasarsa irin wannan shirin wanda zai lakume dalar Amurka miliyon $100 amma bayan da ma’aikatar kiwon lafiyar kasar ta gudanar da bincike aka kuma kawo shi gaban majalisar dokokin kasar gwamnatin kasar take amincewa da tsaron saboda kiyaye diyaucin kasar.