Mali : Sojoji sun murkushe harin ta’addanci a Sansanonin Sojoji da dama

Sojojin Mali sun sanar da cewa “kungiyoyin ‘yan ta’adda ” sun kai hari kan wurare da sansanonin sojojin kasar da dama ciki har da Bamako,

Sojojin Mali sun sanar da cewa “kungiyoyin ‘yan ta’adda ” sun kai hari kan wurare da sansanonin sojojin kasar da dama ciki har da Bamako, Kati, Gao, Kidal, Sévaré.

Hukumomi sunyi kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu da kuma taka tsantsan.

Rundunar Sojin Mali (FAMa) ta sanar cewa ta dakile yunkurin kai hare-hare a birane da dama a fadin kasar.

A cikin wata sanarwa, sojojin sun ce “kungiyoyin ‘yan ta’adda masu dauke da makamai” sun yi yunkurin kai hari kan wasu wurare kafin su sha “mummunan kashi” a hannun FAMa.

A cewar rundunar sojin Mali, an kashe ‘yan ta’adda da dama kuma an lalata kayan aiki.

Rundunar Sojin Mali (FAMa) ta ba da rahoton hare-hare a kan “wasu wurare da bariki a babban birnin da kuma cikin kasar.

Ba a dai fitar da cikakken bayani game da adadin wadanda suka mutu ba.

Duk da haka, rundunar sojin ta jaddada bukatar dogaro da hanyoyin hukuma don samun ingantattun bayanai.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted