Kasahen Mali da Burkina Faso sun sanar da sanya takunkumin shiga ga kasashensu ga ‘yan Amurka a matsayin maida martini ga Washington.
Matakin kasashen na zuwa ne makonni biyu bayan da Washington ta jera wadannan kasashe biyu a cikin jerin kasashen da aka hana shiga Amurka.
A cikin sanarwowin da suka fitar daban daban, ma’aikatun harkokin waje na Mali da Burkina, daga cikin kasashe uku na hadakar kasashen Sahel (AES), sun sanar da cewa za su yi amfani da “matakai iri daya” ga ‘yan Amurka kamar yadda Amurka ta yanke shawara.
Dama tun tuni mahukuntan Jamhuriyar Nijar sun dau irin wannan matakin na mayar da martani ga Amurka inda suka dakatar da bada biza ga duk wani Ba’amurke da ke son zuwa Nijar.
Nijar ta ce ta dau wannan matakin ne don bayyana karfin iko da ‘yancin kasar, kuma diflomatsiyarta ba za ta dinga mika kai bori yana hawa ga kowace kasa ba.
Nijar ta dakatar da bayar da biza dindindin ga dukkan ‘yan aksar Amurka kuma ta hana dukkan Amurkawa shiga kasarta sai abin da hali ya yi inji sanarwar.
A ranar 16 ga watan Disamna ne Amuraka ta sanar da fadada kasashen da ta haramta wa jama’arta shigar kasarta da suha da kasashen kawancen sahel na Mali, Burkina da Nijar.
Amurka ta bayyana daukar wannan matakin na dakatarwa na dindindin ga masu neman bizar gudun hijira ko gajeren zama a kasar bias a cewar gwamnatin Trump ” rashin isassun bayanan tantancewa” saidai ba tare da bayyana me ya sa hakan ya shafi kasashen AES ba.