Wani malamin Ahlul-Sunna ya jaddada cewa: Goyon bayan al’ummar Lebanon ga kungiyar gwagwarmayar Musulunci da sojoji ya hana makiya cimma burinsu
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, babban sakataren kungiyar “Umma Movement” a kasar Lebanon, Sheikh Abdullah Jabri, ya jinjinawa al’ummar Lebanon bisa goyon bayan da suka nuna wa ‘yan gwagwarmayar kasar da kuma sojojin Lebanon, yana mai nuni da cewa wannan hadin kai a lokacin yakin da ya gabata ya hana makiya yahudawan sahyoniya cimma burinsu na neman fadada mamayarsu kan kasar Lebanon.
Sheikh Jabri ya jaddada muhimmancin gwagwarmaya a dukkan bangarori, musamman irin tsayin daka da jarumtaka na ‘yan gwagwarmaya suka nuna a Khiyam, Aita al-Shaab, da sauran garuruwan da suke makwabtaka da kan iyakar Falasdinu da aka mamaye, wanda hakan ya kare kasar Labanon daga masifu da dama da kuma dakile ci gaban sojojin makiya.
Sheikh Jabri ya yi imani da cewa: Wadanda suke kokarin raba kan al’umma ta hanyar kunna wutar sabanin mazhaba ko kabilanci da sabanin addini don raunana karfin al’ummar kasar, wannan wani mummunan yunkuri ne na shafe tarihin Lebanon mai girma tare da malamanta da mayakanta, kuma mugun nufinsu ya gaza a lokacin da yahudawan sahayoniya suka farma kasar Lebanon a baya, kuma a yanzu bakar aniyarsu ba ta cimma nasara ba.