Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa makiya sun canza yanayin matsain lambar zuwa bangaren tattalin arziki bayan da suka kasa cimma nasara a bangaren Soji da ya auna rayuwar iraniyawa fararen hula.
Da yake Magana a wani buki da aka gudanar a birnin Isfahan, babban jami’in diplomasiyan ya ce makiya sun juya da takunkumi da matsin tattalin arziki bayan sun fahimci cewa mutane iran suna tsaye kyam,
Yace a fahimta ta bayan da makiya suka fahimci cewa alummar iran sun tsaya kyam , shi yasa yanzu suka tunkari rayuwar mutane fararen hula, yace suna son cimma manufofinsu ta hanyar takunkumin tattalin arziki da suka kasa cimmawa ta hanyar matakin soji,
Daga karshe ya nuna cewa babban sirrin cin nasarar juyi da kuma cin nasarar alummar iran ko wannne lokaci ya dogara ne da tsayin daka, acikin yanayi mai tsanani da rikice-rikice, amma alummar da ta yi nasara itace wadda tayi tsayin daka kuma ba ta yi watsi da ka’idodinta da mutuncinta ba.