An ji karar tashin boma-bomai a wani kamfanin kera makamai da ke birnin Balikesir a arewa maso yammacin kasar Turkiyya, kuma mutane akalla 12 ne suka rasa rayukansu.
Fashewar ta auku da misalign karfe 08.25 a lokacin kasar. Ministan harkokin cikin gida na kasar Ali Yerlikaya ya ce hatsarin ne ya auku, kuma ba zagon kasa bane, kuma ayyukan ta’addanci ba.
Gwamnatin ta bayyana cewa an dauki matakan da suka dace don ceton ma’aikata da kuma kawo karshen gobarar da ta taso sanadiyyar Fashewar.