Majiyar mayakan kungiyar Hizbulla ta kasar Lebanon ta bayyana cewa dakarun kungiyar sun cilla makamai masu linzami kan wasu wurare a arewacin kasar Falasdinu da aka mamaye da kuma Haifa.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa makamai masu linzami samfurin Fadi-1 da kuma fadi-2 sun fada kan matsugunan yahudawan da ke garin Kiryatshimona wanda yake cikin yankunan da HKI ta mamaye a shekara 1948, kuma sun yi haka ne saboda hare haren da jiragen yakin HKI suke ci gaba da kaiwa a kan yankuna daban daban na kasar Lebanon, inda take kashe fararen hula mafi yawansu mata da yara.
Majiyar kungiyar ta bayyana cewa ta yi amfani da makamai masu linzami samfurin Fadi-1 da Fadi-2 kan sansanin sojojin sama na HKI mai suna Megiddo, da ke kudancin Afula, da kuma sansanin sojojin sama na Ramat David kusa da birnin Haifa.
Banda haka dakarun Hizbullah sun kai hare hare kan masana’antar makamai na Zikhron. Kungiyar ta kara da cewa kafin ta kai wadan nan hare haren dai, ta tura jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa kimani 180 suka bi ta kan sararen samaniyar yankin don fadakar da mutane kan cewa akwai wasu sabbin hare hare na zuwa.
Banda haka majiyar kungiyar ta kasa da cewa makamai masu linzamin nata sun fada kana rumbun ajiyar makamai na runduna ta 146th na sojojin HKI dake Naftalin.
Majiyar HKI ta tabbatar da cewa fiye da makamai masu linzami 50 ne suka fada kan waurare daban daban a cikin arewacin kasar Falasdinu da aka mamaye daga kuma kungiyar Hizbullah a yau Talata.