Majiyoyin Iran Sun Musanta Da’awar Karya Kan Neman Ziyarar Amurka Zuwa Cibiyoyin Sojojinta

Majiyoyin watsa labaran Iran sun musanta da’awar cewa: Amurka ta bukaci ziyarar cibiyoyin sojojin Iran Wasu majiyoyi masu tushe sun musanta ingancin da’awar jita-jita na

Majiyoyin watsa labaran Iran sun musanta da’awar cewa: Amurka ta bukaci ziyarar cibiyoyin sojojin Iran

Wasu majiyoyi masu tushe sun musanta ingancin da’awar jita-jita na baya-bayan nan game da bukatar Amurka ta neman ziyartar cibiyoyin sojojin Iran, tare da bayyana su a matsayin maganganu marasa tushe.

A cewar kamfanin dillancin labarai na Tasnim, rahoton da ya shafi bukatar Amurka na ziyartar wuraren soji, cibiyar makamashin nukiliya da kuma wuraren bincike na Iran cikin makonni masu zuwa, labarai ne marasa tushe ballantana makama.

Haka zalika majiyoyin sun musanta ikirarin da ake dangantawa da ministan harkokin wajen Iraki na cewa “ya yi kira ga Iran da ta fice daga Iraki,” suna masu jaddada cewa ba a taba yin irin wadannan kalamai ba.

Tun da farko dai rahotanni sun da’awar cewa: Amurka ta bukaci Iran da ta bata damar kai ziyara tare da duba wuraren bincike na sojojin Iran guda 31, da cibiyoyin makamashin nukiliya a cikin makonni masu zuwa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments