Majiyar Diplomasiyya: Rasha Ba Ta Gabatarwa Da Iran Batun Dakatar Da Tace Sanadarin Uraniumu Ba

 Kamfanin dillancin labarun “Mehr” na Iran ya nakalto cewa; Iran ba za ta amince da duk wata shawara akan ta dakatar da tace sanadarin Uranium

 Kamfanin dillancin labarun “Mehr” na Iran ya nakalto cewa; Iran ba za ta amince da duk wata shawara akan ta dakatar da tace sanadarin Uranium ba wanda halartaccen hakkinta ne.”

A jiya Asabar ne majiyar diplimasiyyar jamhuriyar musulunci ta Iran ta sanar da tashar talabijin din ‘almayadin’ cewa; Tace sanadarin Uranium a cikin kasarta hakkinta ne halartacce, kuma babu sauyi a cikin matsayar Rasha dangane da haka.”

Wata majiyar Rasha ta ce, gabanin harin HKI akan Iran, a lokacin da ake tattaunawa a tsakanin Iran da Amurka, Moscow ta amince da a fitar da tataccen Uranium sama da daraja 3.67% daga cikin kasar Iran zuwa Rasha a matsayin bayar da tata gudunmawar na warware sabani.

A ranar 20 ga watan Yuli ne shugaban kasar Rasha, Vladmir Putin ya bayyana cewa kasarsa tana goyon bayan Iran a fafutukar da take yin a kare halartattun manufofinta, a su ka hada da mallakar makamashin Nukiliya na zaman lafiya.

A ranar 11 ga watan Yuni kuwa, mataimakin ministan harkokin wajen Rasha Segey Riyabkov, ya bayyana cewa kasarsa a shirye take ta karbi Uranium mai yawa domin taimakawa a cimma yarjejeniya a tsakanin Iran da Amurka.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments